12 Yuni 2019 - 10:12
Isra'ila Ta Kame Wani Babban Kusa Na Hamas

Bangaren kasa da kasa, jami'an tsaron Isra'ila sun kame wani kusa a kungiyar gwagwarmayar falastinawa ta Hamas.

(ABNA24.com) Bangaren kasa da kasa, jami'an tsaron Isra'ila sun kame wani kusa a kungiyar gwagwarmayar falastinawa ta Hamas.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, a jiya ne jami’an tsaron gwamnatin yahudawan suka kai samame a  gidan Ra’fat Nasif, daya daga cikin manyan jagorin kungiyar Hamas, a garin Tulkaram da ke gabar yamma da kogin Jordan.

Rahoton ya ce jami’an tasron gwamnatin yahudawan sun tafi da Ra’fat wani wuri da ba a sani ba.

Tun kafin wannan lokacin dai Isra’ila ta sha kama Ra’afat tana tsare a gidan kaso, inda ya kwashe kimanin jimillar shekaru 18 a gidan kason Isra’ila, kamar yadda a halin yanzu ma suka sake kame shi ba tare da tuhumarsa da aikata wani laifi ba.



/129